An rantsar da Bola Tinubu, mai shekara 71, a matsayin sabon shugaban Najeriya

An rantsar da sabon shugaban Najeriya, ƙasa mafi yawan al’umma da girman tattalin arziƙi a nahiyar Afirka.

Bola Tinubu, mai shekara 71, shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a watan Fabarairun 2023, tare da alƙawarin haɓɓaka ƙasar – duk da cewa akwai jan aiki a gabansa.

Ya karɓi mulki daga shugaba Muhammadu Buhari, yayin da ƙasar ke fama da tashin farashin kayan masarufi da ƙalubalen tattalin arziƙi da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Yanzu haka ƴan takara na jam’iyyar adawa na ƙalubalantar zaɓen a kotu.

Sun bayyana cewa an yi maguɗi a zaɓen.

Leave a Reply