A ranar litin 27 ga watan satumbar 2021, mai girma Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje zai gabatar da takardar nadin da aka yiwa Aliyu Ibrahim Abdulkadir a matsayin sabon sarkin Gaya.
Sanarwa nadin ya biyo bayan wani taron manaima labarai da Sakataren gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji Waziri Gaya ya kira a ranar Lahdi, inda yace gwamnan ya amince da nadin sabon sarkin ne kamar yadda yake kunshe a cikin dokokin masarautu da aka yiwa gyaran fuska a shekarar 2020 wacce ta baiwa gwamnan cikakkiyar damar nadawa ko sauke sarki.
Tsohon Sarkin na Gaya Marigayi Alhaji Ibrahim Abdulkadir ya rasu ne a yan kwanakin da suka gabata sakamakon wata gajeriyar rashin lafiya yana da shekaru 91 da haihuwa.