An nada Mbappe kyaftin din Faransa, madadin Lloris

An bai wa Kylian Mbappe mukamin kyaftin din tawagar Faransa, domin maye gurbin Hugo Lloris.

Bayan da aka kammala gasar kofin duniya a Qatar a 2022, wanda Argentina ta lashe, Faransa ta yi ta biyu, Lloris ya yi ritaya.

Dan kwallon Paris St Germain, mai shekara 24 ya amince ya karbi mukamin, bayan da ya tattauna da kociyan tawagar, Didier Deschamps.

Zai fara sa kyaftin ranar Juma’a a wasan neman gurbin shiga Euro 2024 a karawa da Netherlands.

Karon farko da tawagar Faransa za ta buga tamaula tun bayan kammala gasar kofin dunuya a birnin Doha a Qatar ranar 18 ga watan Disambar 2022.

Golan Tottenham, Hugo Lloris ya yi ritaya, bayan da Argentina ta doke Faransa ta lashe kofin duniya a fenariti, bayan da suka tashi 3-3.

Dan kwallon Atletico Madrid, Antoine Griezmann shine aka bai wa mataimakin kyaftin, bayan da dan wasan Manchester United, Raphael Varane ya yi ritaya.

An dade ana alakanta Mbappe da cewar shine za a bai kyallen kyaftin din tawagar Faransa, wanda ya ci kwallo uku rigis a wasan karshe.

Ya bayar da gudunmuwar da Faransa ta lashe kofin duniya a Rasha a 2018, lokacin yana matashi, wanda aka yi hangen zai zama fitatce a tamaula a lokacin.

Wanda aka haifa a Paris, tsohon dan kwallon Monaco, shine mataimakin kyaftin a PSG, bayan Marquinhos mai jan ragamar ‘yan wasa.

Mbappe ya ci kwallo 19 a wasa 24 a Ligue 1 a kakar nan da bayar da bakwai aka zura a raga a wasannin da PSG ta buga a Champions League.

Bayern Munich ce ta yi waje da PSG a gasar zakaru Turai ta bana a zagayen ‘yan 16, inda aka ci kungiyar Faransa gida da waje.

Leave a Reply