An kashe yan Nigeria tara a harin Kasar Libya

‘Yan Najeriya tara ne cikin akalla mutum 53 da aka kashe a harin da aka kai ta sama kan wata cibiyar tsare ‘yan ci-rani da ke Libya, wanda duniya ta yi Alla-wadai da shi.

Binciken farko-farko na jami’an diflomasiyyar Najeriya da suka ziyarci cibiyar a yankin Tajoura ya tabbatar cewa ‘yan kasar tara ne suka mutu a wannan hari.

Ma’aikatar wajen ta ce tana jiran jerin sunayen mutanen da ke cibiyar domin tabbatarwa ko akwai karin wasu ‘yan Najeriyar da harin ya ritsa da su.

Ta kuma bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa da nufin hukunta masu hannu a wannan aika-aika.

A gefe guda kuma shugaban kasa, Muhd Buhari yayi tur da harin inda yace rashin tausayi ne.

Ita kuwa, shugabar hukumar kula da harkokin yan Nigeria mazauna ketare, Abike Dabiri Erewa, ta mika sakon jaje ga iyalan yan Nigeriar tara da abin ya shafa.