‘Yan bindiga sun hallaka Dr Chike Akunyili, miji ga tsohuwar Shugabar Hukumar da ke kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC kuma tsohuwar ministar yada labarai, marigayiya Farfesa Dora Akunyili.
An kashe shi ne tare da wasu mutane bakwai yayin wani hari da ‘yan bindiga suka kai garin Nkpor da ke karamar hukumar Idemili a jahar Anambra.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa a yayin kai harin maharan sun yi ta fadin cewa ba za a yi zaben Anambra ba a watan Nuwamba. ba
Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar Anambra, DSP Ikenga Tochukwu ya ce har yanzu ba su gama tattara bayanai kan harin ba.
Ana samun rahotannin hare-hare a yankin kudancin kasar nan musamman yankunan da kungiyar masu rajin ballewa daga Najeriya ta IPOB suke.