Masu ruwa da tsaki na lamuran masana’antu da kasuwanci a Najeriya sun taru a Abuja don kaddamar da tambarin bude tashar sauke hajar teku ta Kano da ke Dala mai taken tashar “TSANDAURI”
KANO, NIGERIA – Taron karkashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya samu halartar mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, dan kasuwa Abdulsamad Isiyaka Rabiu da sauran su.
Gwamna Ganduje ya ce tashar za ta kara buda lamuran kasuwanci na jihohin arewa kasancewar tarihin cinikayya a Kano tun lokacin da a ke shigo da kaya da fatauci ta hanyar Sahara daga Afurka ta arewa da ta zama kofar shiga nahiyar turai.