An gurfanar da mutumin da ake zargi da yi wa ‘yar shekara hudu fyade a kotu a Kano

An gurfanar da wani mutum a gaban wata kotun majistare a ke Kano bisa zargin sa da yi wa wata yarinya yar shekara hudu fyade, abin da kuma yayi sanadiyyar mutuwarta.

Iyayen yarinyar sun yi zargin cewa fyaden da aka yi mata ne yayi sanadin mutuwarta.

Sai dai har yanzu ana jiran rahoton likita da zai yi bayani kan abin da ya yi sanadiyyar mutuwarta.

Yayin da aka gurfanar da mutumin mai shekara kimanin arba’in a gaban kotun, lauyoyin gwamnati masu gabatar da kara sun shigar da tuhuma daya, inda aka karanto masa cewa ana zarginsa da yi wa yarinyar ‘yar shekara hudu fyade cikin watan jiya a unguwar Kwana hudu cikin karamar hukumar Nasarawa. Barista Bello Isa Lawan shi ne lauyan gwamnati da ya jagoranci gabatar da wannan tuhuma, ya kuma bayyana cewa ”An kawo shi kotu, an kuma karanta masa abinda ake tuhumarsa da shi , wanda shi kuma ya musa wannan tuhuma da ake yi masa, to shi ne muka gaya wa kotu cewa muna so a ba mu watarana, domin abinda ake zarginsa da shi , abu ne mai girma wanda ita wannan kotun ba ta da hurumin sauraron wannan shari’a, to mun karbi kundin tuhumar kuma za mu kai wa babban jami’in shigar da kara, zai zauna ya yi nazari domin ganin abin da ya kamata a yi, domin yi wa kowanne bangare adalci.”

Leave a Reply