An gano gawar Amurkawa biyu waɗanda aka yi garkuwa da su a Mexico
Biyu daga cikin Amurkawa huɗu da aka yi garkuwa da su a makon da ya gabata a ƙasar Mexico sun mutu, yayin da aka kuɓutar da biyu da ransu, tare da mayar da su Amurka, kamar yadda jami’an Amurka da na Mexico suka bayyana.

A ranar 3 ga watan Maris ne wasu mutane ɗauke da makamai suka yi garkuwa da Amurkawan huɗu yayin da suke cikin motarsu a kan hanyar zuwa birnin Matamoros na jihar Tamaulipas da ke arewa maso gabashin Mexico a kan iyakar jihar Texas.
Wani makusancinsu ya ce mutanen, sun je mexico ne domin tiyatar kwaskwarimar jiki.
Kakakin majalisar tsaron fadar White House John Kirby ya ce: ”Muna miƙa sakon ta’aziyarmu ga iyalai da ‘yan uwan waɗanda suka mutu a wannan hari”.
Babban lauyan gwamnatin Mexico Irving Barrios Mojica ya ce tuni aka mayar da mutum biyu da ke raye zuwa Amurka ranar Talata tare da haɗin gwiwar ofishin jakadancin Amurka da ke ƙasar.
An dai mayar da su Amurka ne cikin tsattsauran rakiyar jami’an tsaron Mexico.
A wata sanarwa da ta fitar hukumar binciken manyan laifuka ta FBI ta tabbatar da mutuwar mutum biyu tare da mayar da biyu da ke raye ƙasar domin yi musu magani a asibiti.
“Ɗaya daga cikin waɗanda ke rayen ya samu munanan raunuka a lokacin harin,” in ji FBI.
Jami’an Amurka sun bayyana sunayen mutane da suka mutu, Zindell Brown da kuma Shaeed Woodard.
Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar za ta yi aiki da hukumomin ƙasashen waje da jami’an tsaro domin farauto waɗanda suka aikata laifin.
Mutane huɗun na tafiya ne a daidai Matamoros – birnin da ke da yawan jama’a kusan 500,000, wanda kuma ke kusa da kan iyakar jihar Texas – a cikin wata ƙaramar mota mai ɗauke da lambar jihar North Carolina a lokacin da wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka buɗe wa motar wuta, kamar yadda FBI ta bayyana.
Wasu bidiyoyi da aka yaɗa sun nuna lokacin da maharan ɗauke da muggan makamai, ke shigar da mutanen cikin wata mota ƙirar A-kori-kura.
An ga ɗaya daga cikinsu na shiga motar da kansa, yayin da sauran kuma ba sa cikin hayyacinsu, inda maharan suka riƙa jansu domin shigar da su motar.
A wani taron manema labarai da suka gudanar ranar talata, jami’an Mexico sun tabbatar da kama wani matashi mai shekara 24, tare da gano Amurkawan huɗu a wani ɗakin katako a wajen birnin na Matamoros.
Jami’an sun ce an yi ta sauya wa mutanen wuri, daga ranar Juma’ar da aka sace su zuwa ranar Talata da aka gano su, domin a rikitar da masu bincike.
Rahotonni sun ce ɗaya daga cikin waɗanda suka ji raunuka mai suna McGee Burgess ta je garin ne domin a yi mata tiyatar kwaskwarimar jiki domin rage ƙiba.
Mahaifiyarta mai suna Barbara Burgess ta shaida wa kafar yaɗa labarai ta ABC cewa sai da ta hana ‘yar tata yin tafiyar, amma ta ƙeƙashe ƙasa.
Birnin Matamoros na cikin jihar Tamaulipas, ɗaya daga cikin jihohin Mexico shida da ma’aikatar tsaron Amurka ke shawartar ‘yan ƙasar su guji ziyarta, saboda ”miyagu da masu garkuwa da mutane”.
To sai dai mazauna kan iyakar Amurka da dama na zuwa garin musamman don neman magani.
Birnin Matamoros na ɗaya daga cikin birane mafiya hatsari a ƙasar, inda dillalan miyagun ƙwayoyi ke iko da mafiyawa yawan yankuna a jihar ta Tamaulipas, kuma suke da ƙarfin iko fiye da na jami’an tsaron ƙasar