An bukaci hadin kan iyaye a karamar hukumar Warawa wajen aikin allurar rigakafin cutar shan inna

An shawarci iyaye a karamar hukumar Warawa, da su bayar da cikakken goyon bayan su ga shirin allurar rigakafin cutar shan inna ta Polio, domin kawar da barazanar kamuwa da cututtuka a tsakanin al’ummar yankin.

Shugaban karamar hukumar, Alhaji Yusuf Abdullahi Danlasan, shi ne yayi wannan kira yayin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan shirin allurar rigakafin cutar ta Polio a ofishinsa.

Da yake jawabi, wakilin hakimin karamar hukumar Warawa, ya roki dagatai da masu unguwanni da su ci gaba da fadakar da mutanensu kan muhimmancin shirin allurar rigakafin cutar shan inna.

Babban jami’in hukumar kula da lafiya a yankin, Danjuma Abudlhadi, yayi bayanin cewa za’a fara shirin ne a yau Asabar, inda yayi kira ga jami’an lafiya da suyi aiki tukuru domin cimma nasarar aikin da aka sanya a gaba.

A jawabinsa, jami’in wayar da kan al’umma a fannin kiwon lafiya, ya yabawa gwamnatin jiha da ta karamar hukumar hadi da kungiyoyi masu zaman kansu, kan nuna kulawarsu ga tsarin kula da lafiyar al’ummar yankin.

Leave a Reply