An ayyana Litinin da Talata ranakun hutu a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Litinin 26 ga wata da ranar Talata 27 ga watan Disamba a matsayin ranar hutun bikin Kirsimati a fadin kasar.

Sanarwar da ma’aikatar cikin gida ta fitar dauke da sa hannun minista Ogbeni Rauf Aregbesola a madadin gwamnatin kasar, ta ce ranar Litinin 2 ga watan Junairun 2023 ne ya kama ranar hutun sabuwar shekara.

Aregbesola ya yi amfani da wannan dama wajen taya mabiya addinin Kirista a daukacin Najeriya murnar bikin Kirsimati da suke gudanarwa duka shekara, domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Isa AS.

Ya bukaci su yi koyi da kyawawan halayaensa da littafin Bibble ya sanar da suka hada da hakuri, da kyautatawa da koyarwa da taimako da sauransu.

Ogbeni Rauf Aregbesola ya tunatar da daukacin ‘yan Najeriya da ke shirin bikin sabuwar shekara, cewa shekarar 2023 ne za a yi babban zaben kasar, don haka su zama cikin shirin kada kuri’a da zaban shugaban da ya cancanci tsamo kasar daga matsin tattalin arziki da inganta da tsaro da ilimi da lafiya.

Leave a Reply