An ƙi bayar da gawar wani mutum a asibiti kan zargin ‘yan uwansa da dukan likita

Hukumomin asibitin koyarwa da ke Ilorin a jihar Kwara ta tsakiyar Najeriya sun ƙi bayar da gawar wani mutum da ya mutu tare da kama ɗaya daga cikin ‘yan uwan mamacin bisa zargin lakaɗa wa wani likitan asibitin duka.

Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa uku daga cikin ‘yan uwan mamacin mai suna Alhaji Saliu ne suka doki wani likita a sashen kula da masu buƙatar kulawar gaggawa na asibitin.

Saboda abin da suka kira ‘rashin kula’ da lilitocin suka nuna musu lamarin da a cewarsu ya sa ɗan uwan nasu ya mutu.

Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan rasuwar ɗan uwan nasu wanda ke fama da cutar sankarar jini.

Ɗaya daga cikin ‘yan uwan mamacin ya ce asibitin ya hana su gawar mamacin saboda faruwar lamarin.

Ya ƙara da cewa sun kai ɗan uwan nasu sashen kula da masu buƙatar kulawar gaggawa na asibitin wajen ƙarfe biyar na asubahin ranar Talata, kuma babu likitan da ya zo kan ɗan uwan nasu duk kuwa da irin roƙon da suka riƙa yi wa likitocin.

Shugabar ƙungiyar likitoci reshen asibitin Mrs Mrs. Elizabeth Ajiboye ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa ”gamayyar ƙungiyar likitoci ta ƙasar ne suka umarci hukumomin asibitin da kada su bayar da gawar mamacin har sai an kama tare da gurfanar da mutanen da suka daki likitan a gaban kotu”.

Daga ƙarshe ta shawarci al’umma da su guji ɗabi’ar cin zarafin ma’aikatan lafiya.

Leave a Reply