Amurka za ta bayar da ƙarin tallafin dala miliyan biyar ga Najeriya domin taimaka wa waɗanda ambaliya ta shafa

Ƙasar Amurka za ta bayar da ƙarin tallafin dala miliyan biyar domin taimaka wa yankunan da ambaliya ruwa ta shafa a faɗin Najeriya.

Tallafin ƙari ne kan dala miliyan ɗaya da hukumar bayar da tallafi ta ƙasar Amurka ta bayar domin taimaka wa waɗanda ambaliya ruwa ta shafa a ƙasar.

Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ya sauka a daminar bana ya shafi fiye da mutum miliyan 4.4 a faɗin ƙasar, lamarin da ya raba mutum akalla miliyan 2.4 da muhallansu, tare da lalata dubban gidaje. Inda kuma sama da mutum 660 suka rasa rayukansu.

Leave a Reply