Amurka ta taya Tinubu murnar cin zaɓe

Ƙasar Amurka ta taya Bola Tinubu murnar cin zaɓe a matsayin zaɓaɓɓen shugaban Najeriya a zaɓen da aka kammala.

Amurkar ta ce wannan zaɓe da aka fafata, ya kawo wani sabon lokaci na siyasa da kuma ci gaban dimokuraɗiyya.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurkan ta yi kira ga hukumar zaɓe da ta ƙara kaimi wajen inganta yanayin zaɓuka masu zuwa na ranar 11 ga watan Maris, inda ta ce ta lura da batun kura-kurai da aka samu a zaɓen shugaban ƙasa.

Har ila yau, Amurkan ta buƙaci jam’iyyu da su guji yin kalamai ko abubuwa da za su tayar da hankali a wannan lokaci, inda ta ce ta su bi hanyar da ta dace wajen bin hakkinsu.

Leave a Reply