Amurka ta ce Najeriya ta gurfanar da mutanen da suka aikata laifukan zaɓe

Amurka ta yi kira ga hukumomin Najeriya su tabbatar, sun gurfanar da mutanen da aka samu da hannu, ko waɗanda suka ba da umarnin a razana masu zaɓe ko suka daƙile harkar zaɓen gwamnoni a ƙasar.

Cikin wani rahoto da Ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya fitar ta ce Amurka ta damu matuƙa kan aika-aikar da aka yi wa masu zaɓe ta hanyar razanarwa da daƙile yin zaɓe a jihohi irinsu Kano da Lagos.

Amurka na wannan kira ne a matsayin wani martani ga zaɓen ranar Asabar da ta wuce na gwamnoni da ‘yan majalisun dokokin jihohin ƙasa

Haka kuma Amurkan ta ce ita ma za ta yi nazari a kan dukkan matakan ladabtarwa da take da su, ciki har da ƙarin hana bizar shiga ƙasarta ga mutanen da aka yi imani suna da alhaki, ko an haɗa baki da su wajen yin zagon ƙasa ga tsarin dimokraɗiyyar Nijeriya.

Ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya ce jami’an diflomasiyyar Amurka da suka sa-ido kan zaɓuka a Lagos da sauran wurare sun ga irin waɗannan kura-kurai da idanuwansu.

Sanarwar ta ce amfani da kalaman ƙabilanci a lokacin zaɓen gwamnan Lagos, musamman abin damuwa ne.

Ta yaba wa duk ‘yan siyasar Nijeriya da shugabannin addinai da na al’umma da matasa da ‘yan ƙasar, waɗanda suka zaɓi bijire wa waccar hanya, kuma suka nuna adawa a kan irin waɗannan kalamai na ta da hankali da tunzura rikici, abin da ke tabbatar da ƙudurin ‘yan ƙasar wajen mutunta tsarin dimokraɗiyya.

Sanarwar ta ce bayan zaɓukan shugaban ƙasa na 25 ga watan jiya, Amurka ta bi sahun masu sa-ido na ƙasashen waje, wajen yin kira ga hukumar zaɓe ta gyara kura-kuren da aka samu a tsare-tsaren yin zaɓe da kuma amfani da na’urori.

Kuma ga alama zaɓukan da suka wuce, sun nuna an samu gagarumin ci gaba, don kuwa akasari an buɗe rumfunan zaɓe a kan lokaci kuma an ga sakamakon zaɓe da yawa a shafin latroni da ke nuna sakamakon da aka wallafa a kan lokaci.

Sanarwar ta sake yin kira ga duk masu ƙorafe-ƙorafe game da zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jiha, su bi kadi ta hanyoyin da doka ta tanada, waɗanda kuma lallai ba za a yi musu katsalandan ba.

Sanarwar ta sake yin kira ga al’ummar Nijeriya su haɗa kai wajen aiki tare kamar yadda suka shiga aka dama da su a zaɓen sabbin shugabanni kuma su ci gaba da ƙoƙari wajen ƙarfafa tsarin dimokraɗiyyar ƙasar mai cike da kuzari.

Article share tools

Leave a Reply