Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya bayyana takaicin sa kan zubar da shara.

Shugaban kwamitin karta kwana na kwashe sharar jihar Kano Ambassador Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya bayyana takaicin sa bisa yadda wasu marasa kishin cigaban Kano suke cigaba da jibge shara a titunan birnin jihar nan musamman wuraren da kwamitin sa ya kwashe sharar a kwanakin baya.

Dan zago ya bayyana hakan ne lokacin da kwamitinsa yake gudanar da aikin kwashe sharar da sake jibge a jikin asibitin Murtala daidai dakin masu haihuwa.

Yace abin takaicin shine yadda wajen da ake zubar da sharar yake da alaka ta Kai tsaye da babban dakin haihuwa na asibitin.

Wasu daga cikin matan dake kwance domin haihuwa a asibitin sun bayyana irin halin kuncin da suke fuskanta sanadiyar zuba sharar.

Unguwannin da kwamitin ya ziyarta domin tsaftace su daga tarin sharar a yau sun Hadar Alfindiki, Kasuwar kantin kwari, asibitin Murtala Maternity, Gidan Shattima da sauransu.

Leave a Reply