An zaɓi dan wasa Lionel Messi cikin jerin sunayen waɗanda za su iya kasancewa gwarzon ɗan wasa ‘sabon zuwa’ na gasar Major League Soccer.

Ɗan wasan gaban Argentina, mai shekaru 36, ​​ya koma ƙungiyar Inter Miami ne a watan Yuli.

Ya kuma zura kwallaye 11 a dukkan gasa, inda ya taimaka wa kungiyar ta lashe gasar cin kofin Leagues karo na farko a tarihinta.

Messi ne ake kyautata wa zaton lashe kyautar Ballon d’Or ranar Litinin mai zuwa, bayan ya bada gagarumar gudunmawa ga Argentina wajen lashe gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022.

Miami na cikin wani mawuyacin hali a gasar Major League Soccer a wannan kakar kafin ɗan wasan ya zo watan Yuli, tare da tsofaffin abokan wasan sa na Barcelona Jordi Alba da kuma Sergio Busquets.