‘Akwai yiwuwar darajar naira ta sake faɗuwa a ƙarshen shekara’

Masana harkokin sauyin kuɗi a Najeriya na ganin darajar kuɗin ƙasar naira za ta sake faɗuwa yayin da shekarar 2022 ke ƙarewa, musamman a farashin gwamnati.

An canzar da dala ɗaya kan N457 a farashin gwamnati ranar Alhamis, fiye da N450 da aka canzar da ita a makon da ya gabata.

A kasuwar bayan fage kuwa an canzar da dalar kan N740.

“Shekara ta zo ƙarshe…ba na tsammanin za ta farfaɗo,” a cewar wani ɗan kasuwa a bankin kasuwanci cikin hirarsa da Reuters. “Amma ina ganin za ta zauna yadda take ko ta ɗan faɗi kaɗan.”

Sauya wasu takardun naira a watan nan da kuma rage adadin kuɗin da ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni za su iya cirewa a kullum na ci gaba da ɗumama harkokin kuɗi a Najeriya.

Leave a Reply