Afirka ta Kudu na cikin barazanar fuskantar ƙarancin kaji

Afirka ta Kudu na iya fuskantar ƙarancin kaji sakamakon matsalar wutar lantarki da take fama da shi wadda kuma ke shafar kajin da ake yankawa, a cewar kungiyar masu kiwon kaji ta ƙasar.

Kungiyar ta ce rashin wutar lantarki ya sanya ta rage yawan kaji da take yankawa saboda mayanka ba sa iya adana su saboda ƙarancin wuta.

Kafofin ƴaɗa labarai na cikin gida sun ruwaito kungiyar na cewa ta matsalar ta wutar lantarki ta kai ta ga kasa yanka kaji kusan miliyan 10 a makonni da suka gabata.

Tasirin ƙarancin wutar lantarkin har ya fara shafar kantunan sayar da abinci irinsu KFC, inda ake kyautata zaton cewa lamarin zai iya taɓarɓarewa.

Hakan na zuwa ne bayan wani gargadi na cewa lamarin zai iya ɗaukar tsawon lokaci wadda kuma zai shafi harkokin hada-hadar kasuwanni.

Leave a Reply