Adeleke ya umarci manyan jami’an  kananan hukumomi su karbi ragamar aiki a wajen shugabannin kananan hukumomin da aka sauke

GwamnaAdemola Adeleke na jihar Osun ya umarci  Manyan jami’an kana nan hukumomi da cigaban gundumomi a jihar, da su amshi ragamar gudanar aikace aikace daga shugabannin kananan hukumomi da kansilolin da aka sauke.

Adeleke ya bayar da umarnin ne  a wata takarda mai dauke da sa hannun kakakinsa Malam Olawale Rasheed.

Adeleke ya bayyana cewa; umarnin ya fara aiki ne nan take.

Gwamnan yace daukar matakin yarda ne da hukuncin da babbar kotun Taraiya dake zaman a Osogbo babban birnin jihar ta yanke na sauke shugabannin kananan hukumomi da kansilolin daga mukamansu.

Da yake mayar da martani kan lamarin, shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta Najeriya ALGON reshan jihar Osun, Mista Abiodun Idowu, ya bukaci ‘ya’yan kungiyar da su kwantar da hankulansu su kuma zauna da kowa lafiya.

Leave a Reply