Abin da ya sa EFCC ta yi wa kamfanin Ɗangote dirar mikiya

Bayanai na ci gaba da fitowa kan dirar mikiyar da jami’an hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, suka yi wa ofisoshin gungun kamfanonin Ɗangote da tsakar ranar Alhamis.

Sun dai shafe kusan tsawon sa’a biyu suna duba takardun harkokin kuɗi na kamfanin, a wani ɓangare na bincike kan yiwuwar ɓarnata kuɗaɗen waje musamman dalar Amurka da suka riƙa samu cikin ragwame daga babban bankin Najeriya.

Sun fara dira ofisoshin kamfanin ne tun misalin ƙarfe 11 na safe.

Gungun kamfanonin Ɗangote na hamshaƙin ɗan kasuwar Afirka, Aliko Ɗangote yana da masana’antun sarrafa sumunti da takin zamani da sukari da sauransu. Kuma yana ƙoƙarin fara tace man fetur ganga 650,000 a sabuwar matatar man da ya gina a kan kuɗi dala biliyan 20.

A ƙarƙashin tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, bankin ya ɓullo da tsarin musayar kuɗaɗen waje iri daban-daban da kuma sayar da dala cikin rangwame ga wasu kamfanoni, ciki har da Ɗangote don taimaka musu wajen sayo kayan sarrafawa da suke buƙata.

A watan Yuni ne, hukumomin Najeriya suka kama Godwin Emefiele bayan an dakatar da shi daga kan muƙaminsa, tare da tuhumar sa da laifuka daban-daban ciki har da zargin almundahana.

Wata majiya a kamfanin Ɗangote ta tabbatar da samamen da jami’an EFCC sanye da jajayen falmaran suka kai ofishinsu da ke Lagos.

Yayin da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito hukumar EFCC na cewa binciken da jami’anta suka gudanar a ofisoshin Ɗangote, aiki ne da za a faɗaɗa shi zuwa wasu kamfanoni.

“Mun je babban ofishin Gungun kamfanonin Ɗangote a yau (Alhamis) domin duba takardunsu kan binciken da ake ci gaba da yi game da yiwuwar keta dokokin da suka tsara harkokin kuɗaɗen waje a zamanin mulkin Godwin Emefiele,” kamar yadda Reuters ya ambato wata majiya tana cewa.

“A nan muna magana ne a kan canjin kuɗaɗen waje iri daban-daban da sauransu. Bincike ne da ake ci gaba da yi kuma yanzu aiki ya zo kan kamfanin Ɗangote,” a cewar majiyar.

Ba a kai mana samame ba – BUA

A ɓangare ɗaya kuma kamfanin BUA na AbdusSamad Rabi’u ya musanta cewa jami’an EFCC sun kai samame ofisoshinsa a ranar Alhamis.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Gungun kamfanonin BUA ya ce babu wani jami’i na EFCC da ya kai musu samame kamar yadda wasu kafofi na intanet suka riƙa yaɗawa.

An daɗe ana zargin cewa tsarin canjin kuɗi da Najeriya ke amfani da shi, na ba da damar azrurta wasu tsirarun mutane, yayin da darajar naira ke ci gaba da taɓarɓarewa.

Hukumar EFCC dai zuwa yanzu ba ta fito ta yi ƙarin haske kan wannan bincike da ta ce jami’anta na gudanarwa a ofisoshin kamfanonin sarrafa kayayyaki na ƙasar kamar Ɗangote ba.

Leave a Reply