Abba Gida-gida ya fara ɗaukar matakan binciken gwamnatin Ganduje

Sabon gwamnan jihar Kano Injiniya, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-gida, ya fara daukar matakan binciken tsohuwar gwamnatin da ya gada ta Abdullahi Umar Ganduje, inda hawansa mulki ke da wuya ya bayar da umarni kan wasu tsauraran matakai.

Daga cikin matakan da ya fara dauka gwamnan ya soke dukkanin cinikin da aka yi na sayar da wasu wurar na gwamnatin jihar

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a jawabinsa na bayan rantsuwa gwamnan ya bayar da umarni ga hukumomin tsaro a jihar da su je su karbe iko da wadannan wurare da gwamnatin ganduje ta sayar.

Wasu daga cikin wuraren da aka sayar sun hada da filayen makarantu da na masallatai da makabarta da jikin badala da sauransu.

Matakin ba ya tsaya ga kadarorin gwamnati da ke cikin jihar ba ne har ma wadanda suke waje dokar soke cikin ta shafa.

Gwamnan wanda ya kuma sauke dukkanin shugabannin ma’aikatu da hukumomi da kamfanoni na gwamnati nadin siyasa har ma da hukumomin daraktoci na gudanarwa, da ma’aikatu da hukumomi da kamfanoni har da da manyan makarantun jihar ya kara da cewa dukkanin matakan da zai dauka a kwankin da ke tafe zai yi ne da nufin dawo da kima da martabar jihar.

Leave a Reply