Abba Gida-gida ya buƙaci masu taya shi murna su yi masa addu’a maimakon dogon tattaki

Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya buƙaci masu yin doguwar tafiyar ƙafa domin nuna murnarsu kan samun nasarar zaɓe da ya yi, da cewa su daina.

A maimakon haka ya buƙace su da su yi masa addu’ar samun nasara a mulkinsa domin maido da ƙwarin gwiwar da ‘yan jihar suka rasa cikin shekaru takwas da suka gabata.

A wata sanarwa da zaɓaɓɓen gwamnan ya fitar, mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawunsa Sanusi Bature Dawakin Tofa, Abba ya buƙaci magoya bayansa da ‘yan jam’iyyarsa ta NNPP da su yi masa addu’ar samun nasara a mulkinsa.

Sabon gwamnan ya ce yin addu’a kaɗai ta wadatar wajen nuna murna ga nasarar da ya yi a zaɓen na ranar Asabar, ba sai mutum ya shafe tafiyar kilomitoci masu yawa a ƙafa ba.

Musamman a cewar sanarawar, idan aka yi la’akari da halin rashin tsaro na matsalar ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane, waɗanda ke barazana ga zirga-zirgar jama’a da kayayyaki a faɗin ƙasar.

Yayin da yake gode wa magoya bayansa na ciki da wajen jihar Kano, zaɓaɓɓen gwamnan ya buƙaci masu doguwar tafiyar ƙafa da su daina, domin kuwa a cewarsa hakan ba zai taimaka wajen magance tarin matsalolin da ke jiran sabuwar gwamnatinsa ba, kamar yadda ya bayyana.

A Najeriya dai matasa da dama kan jefa rayuwarsu cikin hatsari wajen yin doguwar tafiyar ƙafa domin taya wani gwaninsu murnar nasarar da ya yi ta lashe zaɓe.

Matsan da a lokuta da dama kan ƙare doguwar tafiyar ba tare da samun ganawa da gwanin nasu ko makusantansa ba.

Leave a Reply