Hukumar kwallon kafa ta Afirka, Caf za ta yi bikin raba jadawalin neman gurbin shiga gasar kofin nahiyar Afirka da za a yi a 2023.
Code d’Ivore ce za ta karbi bakuncin wasannin da za a yi a 2023, bayan da Kamaru ta gudanar da gasar 2020, wadda aka yi a 2022.
Hakan ya biyo bayan cutar korona da ta kawo tsaiko, sannan aka yi gasar tsakanin Janairu zuwa Fabrairun 2022.
Za a raba jadawalin ne a Afirka ta Kudu ranar Talata, inda Thomas Mlambo zai gabatar tare da Solomon Kalou da kuma Lucas Radebe.
Kasashe 48 ne za su fara fafatawa zuwa zagaye na biyu, inda za a raba su zuwa tukunya hudu, kowacce kasa za ta kasance a gurbin da take da shi a jadawalin Fifa, wanda ta fitar ranar 31 ga watan Maris din 2022.
Daga nan za a raba kasashen rukuni 12 dauke da hur-hudu kowanne, wato daga A zuwa L, inda duk wadda ta yi ta daya da ta biyu za ta kai gurbin buga gasar kofin nahiyar Afirka da Code d’Ivoire za ta karbi bakunci a 2023.
Itama Code d’Ivoire za ta kasance cikin kasashen da za a raba jadawalin da ita, duk da tuni ta samu gurbin buga gasar tunda ita za ta karbi bakuncin wasannin.
Kenya da Zimbabwe wadanda Fifa ta dakatar suna daga cikin wadanda za a raba jadawalin tare da su, sai dai kuma idan nan da mako biyu ba a cire takunkumin da aka dora musu ba, za a fitar da su daga buga wasannin neman gurbin shiga kofin Afirka.
Saboda haka a rukunin da suke za su zama uku kenan, kuma ba za a saka su waje daya ba.
Za a fara wasannin cikin watan Yunin 2022.
Rabon da Code d’Ivoire ta karbi bakuncin gasar tun 1984.
Senegal ce ke rike da kofin Afirka, wanda ta lashe a Kamaru, bayan da ta yi nasara a kan Masar.