”A kula da yanda ake mu’amala da wuta” – Hukumar Kashe Gobara Reshen Jihar Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta gargadi al’umma da su  kula da yanda suke mu’amalantar wuta a wannan yanayi da ake ciki domin gujewa tashin gobara, musamman ma  yanzu da ake ci gaba da fuskantar  yanayin sanyi. 

Hukumar tayi wannan jan hankali ne ta bakin Kakakin ta PFS Saminu Abdullahi a cikin rahoton ta da ta saba fitarwa a kowane wata kan nasarorin da ta samu.

Ga cikakken rahoton sanarwar tare da wakilin mu Idris Usman Alhassan. 

Leave a Reply