Real Madrid ta kawo karshen Chelsea mai rike da kofin Champions League, bayan da ta yi nasara da ci 3-2 a Santiago Bernabeu ranar Talata.
Karo na 31 kenan da Real Madrid ta kai daf da karshe a ko dai European Cup ko kuma Champions League, kenan ta bayar da tazarar zuwa sau 11, fiye da kowacce kungiya.
Chelsea ta ci kwallaye ta hannun Mason Mount da Antonio Rudiger da kuma Timo Werner.
Real Madrid ta zura nata a raga ta hannun Rodrygo da kuma Karim Benzema, wanda ya ci kwallo hudu a ragar Chelsea a haduwa biyun da suka yi.
Kungiyar Sifaniya ta kai wasan daf da karshe da cin kwallo biyar da hudu kenan gida da waje a suka kece raini a bana.
A wasan farko da suka buga ranar Laraba 6 ga watan Afirilu, Real Madrid ce ta yi nasara da ci 3-1 a fafatawar da suka yi a Stamford Bridge.
Wannan shi ne karon farko da Chelsea ta buga wasa a filin Real Madrid na Santiago Bernabeu a Sifaniya.
Ko a bara da Chelsea ta ziyarci Real Madrid a gasar Champions League wasan daf da karshe a Estadio Alfredo Di Stefano suka yi wasan.
Wannan shi ne wasa na bakwai da suka kece raini a gasar Zakarun Turai, Chelsea ta yi nasara a wasa uku da canjaras biyu, sai Real da ta ci biyu.
‘Yan wasan da Carlo Ancelotti ya fuskanci Chelsea a Champions League karawar quarter-final a Santiago Bernabeu.