Shugabar Matan PDP Ta Sauye Sheka Kwana 4 Kafin Zaben Gwamna A Sakkwato

Kulu Abdullahi Rabah, wadda aka sani da ’Yar Sardauna ta sauya sheka zuwa APC kwana hudu kafin zaben gwamna

Shugabar mata a jam’iyar PDP ta jihar Sakkwato, Hajiya Kulu Abdullahi Rabah, wadda aka sani da ’Yar Sardauna ta sauya sheka zuwa APC kwana hudu kafin zaben gwamna da za a gudanarwa a ranar Assabar.

Hajiya Kulu Rabah a takardar da ta aike wa shugaban mazabarta a garin Mai Kujera a karamar hukumar Rabah, ta sanar da shi barin jam’iyar saboda rashin fahimtar da ke cikin PDP, lamarin da a cewarta ya hana ciyar da Jihar Sakkwato gaba.

Kulu Rabah, jim kadan da barin PDP ta bayyana shigarta APC a gaban jagoran Jam’iyar APC a jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da dan takarar gwamna, Ahmad Aliyu Sokoto.

Jam’iyyar PDP ne dai ke mulkin Jihar Sakkwato a halin yanzu, sai dai a wannan karo ba gwamna mai ci, Aminu Waziri Tambuwal ba ne dan takararta.

Leave a Reply