2023: Za A Fara Shirye-shiryen Aikin Hajji Ranar 21 Ga Disamba – NAHCON

Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya sanar da cewa, za a fara shirye-shiryen Hajjin shekarar 2023 a ranar 21 ga watan Disamba.

Da yake jawabi a wajen taron masu ruwa da tsakin bayan aikin Hajji na 2022 da aka gudanar a babban masallacin kasa da ke Abuja, Hassan ya ce za a fara shirye-shiryen tsakanin NAHCON da ma’aikatar Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya a ranar.

Ya sanar da cewa NAHCON ta shirya gudanar da aikin Hajjin shekarar 2023 a kan tsarin adashin gata na aikin Hajji da kuma tsarin biyan kudi na yau da kullun.

Ya bayyana cewa taron an shirya shi ne domin hada masu ruwa da tsaki a harkar aikin Hajjin Najeriya da nufin yin nazari tare da duba aikin Hajjin bana tare da samar da mafita don kara inganta aiyukan hukumar a shekara mai kamawa.

Leave a Reply