2023: Ina Da Yakinin Za A Yi Sahihin Zabe – Jega

Tsohon shugaban Hukumar Zabe Mai zaman kanta ta Kasa INEC, Farfesa Atahiru Jega, ya ce yana da yakinin cewa Najeriya za ta gudanar da sahihin zabe a shekarar 2023 duk da kalubalen da take fuskanta.

Jega ya bayyana hakan ne a wajen taron karrama Farfesa Adele Jinaidu da aka gudanar a Abuja.

Ya ce, duk da hare-haren da ake kai wa cibiyoyin INEC da kuma tashin-tashinar yakin neman zaben da ake gani, yana da tabbacin hakan ba zai hana gudanar da ingantaccen zabe ba a shekarar badi ba.

Ya kara da cewa, duk da dai yana ji wa sakamakon zaben tsoro, amma yana da kyakkyawan yakini a kan makomar kasarnan. Kazalika, ya ce duk da abubuwa marasa dadi da wasu shugabannin siyasa ke jagorantar aikatawa, yana fatan tsabtataccen zabe zai samu a Najeriya a shekarar

Leave a Reply