2023: Idan Ka Isa Ka Shirya Tattaki Irin Namu A Kano – Ganduje Ya Kalubalanci Kwankwaso 

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Ganduje, ya kalubalanci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ya gudanar da taron tattaki a jihar domin gwada farin jininsa.

Ganduje ya yi wannan magana ne kan yadda mutane suka yi fitar dango don mara wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu baya a jihar Kano.

A cewar Gwamnan, da yawa daga cikin mabiya Kwankwaso a yanzu suna tare da Jam’iyyar APC.

Gwamna Ganduje ya kara nuna shakku kan batun siyasar Malam Ibrahim Shekarau, wanda ya bayyana cewa yana ficewa daga wannan jam’iyya zuwa wata tare da rasa dimbin mabiyansa a tafiyar siyasa.

Leave a Reply