KUNGIYAR JAMI’AN KIWON LAFIYA SUN NUNA RASHIN GAMSUWA DA TSARIN GWAJIN CUTAR COVID-19

Kungiyar jami’an kiwon lafiya ta kasa ta nuna rashin gamsuwar ta bisa tsarin gwajin da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta gabatar akan cutar Covid 19.

Kungiyar tace duk da cewa akwai akalla mutane dubu 5 da suke dauke da cutar sai dai kawo yanzu tsarin gwajin baya fitar da hakikanin yadda cutar take a kasarnan.

Kungiyar ta jami’an kiwon lafiya ta sanar da matsayar tane a wani jawabi da shugaban kungiyar Dakta Faduyile da babban sakataren kungiyar Dakta Olumiyiwa Odusote suka sanyawa hannu.

Sannan kungiyar ta bayyana mtakin karbar maganin gargajiya na kasar Madagasca da gwamnatin tarayya tayi  a matsayin sanya wakafi a kokarin samo maganin da zai kare rayukan al’ummar kasarnan.