Ɗan Chinan da ake zargi da kashe Ummita ya fara gabatar da shaidu a gaban kotu

A yau ne ɗan ƙasar Chinan nan da ake zargi da kashe budurwarsa mai suna ‘Ummita’ a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ya fara gabatar da shaida a shari’ar da ake yi masa.

Hakan ya zo ne bayan masu ƙara sun kammala gabatar da na su shaidun a gaban babbar kotun jihar.

A zaman babbar kotun na yau, mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya ci gaba da sauraren tuhumar da ake yi wa Mista Geng Quangrong da kashe tsohuwar budurwarsa Ummulkhuksum Sani Buhari wadda aka fi sani da ‘Ummita’.

Mista Geng ya tsaya a gaban kotun a matsayin shaida, ya bayyana wa kotun yadda suka haɗu da Ummulkhuksum inda yace wata ƙawarta ce ta ba ta lambarsa ta kira shi cewa tana ƙaunarsa kuma za ta aure shi, shi kuma ya amince.

Sai dai bayan an ɗauki lokaci suna soyayya tare da kashe mata maƙudan kuɗaɗe sai ta ƙi auren sa, inda ta auri wani amma duk da haka lokaci zuwa lokaci tana kiransa su gaisa ta nemi kuɗi ya ba ta a cewar Mista Geng.

Barista Abdullahi Maji na daya daga cikin lauyoyin da ke kare Mista Geng ya kuma shaida wa BBC cewa ”ya bayyana wa kotun lokacin da suka fara haɗuwa lokacin yana Delta, ta samu lambarsa daga hannun ƙawarta, ta gayyace shi ya zo Kano, sun ha ɗu faga nan kuma sun fara soyayya tsakaninsu.

”Ya yi maganar cewa aƙalla ya kashe mata naira miliyan 60, ta ci kuɗaɗe da yawa daga wajensa, kama daga kuɗaɗen soyen mota da na fili da na fara kasuwancin duka shi ya bata, kuma kamar yadda ya bayyana akwai bayanan kididdigar banki na kuɗin da ya kashe mata, kuma kamar yadda ya faɗa za su tabbatar da haka idan an karɓo su daga banki”, in ji lauyan mista Geng.

Kazalika, Mista Geng ya ci gaba da faɗaw a kotun cewa ya taɓa ba ta naira miliyan 10 ta sayi mota, amma sai ta yi amfani da kuɗin ta sayi fili a Abuja ta fara gini a 2021.

Amma daga ƙarshe saboda ba ta son ta aure shi sai ta ce ba ta karɓi komai daga hannun sa ba.

Har wayau Mista Geng ya shaida wa babbar kotun cewa a ranar 13 Satumba 2022 ta buƙaci ya bata kuɗi ta kammala aikin ginin ta a Abuja.

Inda shi kuma ya faɗa mata cewa ba shi da kuɗi abin da ya fusatata ta dai ɗaukar wayarsa, sannan ya ƙara da cewa duk maganar da suka yi tana cikin WhatsApp dinsa.

Mista Geng yace yana matuƙar ƙaunar Ummulkhuksum, ba ya son ɓacin ranta.

Sannan ya faɗa wa kotun cewa ta rika yin ƙorafin cewa ba ya kashe mata kuɗi kamar baya inda ta tambaye shi ko ba shi da kuɗi ne.

Daga bisani kuma ta faɗa masa cewa ta samu wani mutum da suke soyayya har ma ta aika masa da hotunan sabon saurayinta, al’amarin da ya ba shi haushi.

Ɓangaren masu gabatar da ƙara sun ce suna bibiyar bayanan da Mista Geng yake bayarwa a kotu sau da kafa.

Hajiya Aisha Mahmud darakta ce a ma’aikatar shari’a ta jihar Kano ta yi ƙarin haske bayan fitowa daga kotun.

”Tun wancan zaman da muka ce mu mun rufe sai ya nemi kotu da ta ba shi damar ya sake kirowa shaidunsa, tare da neman kotu da ta sake kirawo shaidun da muka gabatar, inda ka kira mahaifiyar yarinyar ta zo ya yi mata tambayoyi, da ɗan sanda shi ma ya zo ya yi masa tambayoyi”

”Mu ba mu san yawan sahidun da zai kira ba, yau dai ya fara, to sai goben in ya gama kiran shaidun nasa, zai rufe gobe”, inji Hajiya Aisha

Alkalin babbar kotun mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya ɗage zaman kotun zuwa gobe goma sha biyu ga wannan watan don ci gaba da sauraron Mista Geng kan abin da ya faru tsakaninsa da Ummulkhuksum, wadda ake zargin ya kashe ta.

Leave a Reply