‘Ɗaliban manyan makarantun tarayya ne kawai za su fara samun bashin karatu na Najeriya’

Shugaban asusun bayar da bashin karatu na Najeriya, Mr Akintunde Sawyerr, ya ce dalibai miliyan 1 da dubu 200 ne a fadin manyan makarantun gaba da sakandare na gwamnatin tarayya za su samu bashin a kashin farko.
Akintunde ya ce za a fara bude kafar ne ga daliban makarantun tarayya, wadanda makarantunsu suka riga suka kammala sanya bayanan daliban.
A bayanan da ya gabatar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, shugaban ya ce bashin wanda za a ba wa dukkanin daliban manyan makarantun gaba da sakandare na gwamnati, za a bayar da shi ne kashi-kashi inda za a fara da makarantun tarayya kafin a kai ga makarantun gwamnatocin jihohi.
Shugaban ya ce, hanyoyin biyan bashin maras kudin ruwa, suna da sassauci, kuma dalibi zai fara biya ne shekara biyu bayan kammala aikin yi wa kasa hidima idan har ya samu aiki.

Leave a Reply