Ƴan sanda sun kama zaɓabben ɗan majalisar wakilai na NNPP a Kano

Ƴan sanda a jihar Kano sun kama ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Dala a majalisar wakilai ta tarayya, Sani Madakin Gini, wanda aka zaɓa a makon jiya, bisa laifin mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan, inda ya bayyana cewa a yanzu haka ana bincike kan ɗan majalisar.

Kakakin ‘yan sandan ya ce ɗan majalisar yana hannunsu a halin yanzu, kuma suna ci gaba da bincike.

Ya ce ‘yan sanda ba za su yi ƙasa a gwiwa a ƙoƙarin ganin doka ta yi aiki kan kowa da aka kama da laifi.

Kama Sani Madakin Gini da aka zaɓa a karkashin jam’iyyar NNPP ya haifar da damuwa da martani daga bangarori daban-daban.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan kama shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya, Hon Ado Doguwa, wanda ke wakiltar mazaɓar Doguwa da Tudun Wada a jihar Kano, bisa zargin sa da hannu a wata hatsaniyar siyasa da ta yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum uku.

Leave a Reply