Ƴan sanda sun ja hankalin ƴan takarar shugaban ƙasa kan kalaman tayar da hankali

Ƴan sanda a Najeriya sun buƙaci ƴan takarar kujerar shugaban ƙasa da su gargaɗi magoya bayansu kan yin kalaman da za su tayar da hankali a daidai lokacin da ƙasar ke jiran sakamakon zaɓe da aka gudanar wanda ba a taɓa ganin irinsa ba cikin shekaru.

Ƴan sandan sun kuma gargaɗi ‘yan siyasa kan matsa wa hukumar zaɓe kan fitar da sakamakon zaɓe.

An kuma buƙaci ‘yan siyasa da su yi amfani da wannan damar na jiran sakamakon zaɓe da ake yi, wajen bin doka da oda da kuma mutunta kundin tsarin mulki, a cewar sanarwar ‘yan sanda.

Ya zuwa yanzu an sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jiha ɗaya tilo cikin jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.

Leave a Reply