Ƴan bindiga sun sace babban sakatare a ma’aikatar sufuri ta jihar Neja da ke arewacin Najeriya.
An sace Dakta Ibrahim Garba Musa ne da asubahin yau tare da ɗansa, kamar yadda sakatariyar watsa labarai ta Gwamnatin jihar, Mary Noel Berje, ta shaida wa BBC.
Ta ce har yanzu ba su gama tattara bayanai ba game da al’amarin amma ta ce a gidansa da ke Zungeru a ƙaramar hukumar Wushishiƴan bindiga suka abka suka sace shi da ɗansa.
Wasu rahotanni sun ce an sace shi ne gidansa bayan kammala bikin aure.
Wannan na zuwa bayan gwamnatin Neja ta tabbatar da mutuwar sojoji biyu da jikkata wasu da dama a harin da ƴan bindiga suka kai a yankin Kagara.