Ƴan ƙwadago sun yi watsi da albashin naira 48,000 ga ma’aikatan Najeriya

Ƙungiyoyin ƙwadago na Najeriya sun yi watsi da tayin da gwamnatin tarayya ta yi na naira 48,000 a matsayin sabon albashi mafi ƙaranci ga ma’aikatan ƙasar.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ƙwadago ta NLC da TUC suka fitar, sun bayyana tayin na gwamnatin tarayya a matsayin abin ban takaici, da cewa hakan tamkar cin fuska ne ga ma’aikatan Najeriya kuma ya yi ƙaranci idan aka kwatanta da buƙatun da ƙungiyoyin suka gabatar.
A kan haka ne ƙungiyoyin ƙwadagon suka yanke shawarar ficewa daga tattaunawar da ake yi kan mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata, tare da yin kira ga gwamnati da ta sake tunani domin gabatar da tayin da ya fi dacewa domin samun matsaya.
A baya dai ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta gabatar da buƙatar tsayar da mafi ƙarancin albashi a kan naira 615,000.
NLC ta ce ta yi hakan ne la’akari da halin matsin rayuwa da tashin farashin kayan masarufi da al’ummar ƙasar ke fuskanta.

Leave a Reply