ƙungiyoyin ƙwadago sun sake yin fatali da Naira dubu 54 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na Najeriya sun sake yin fatali da tayin mafi ƙarancin albashi na naira dubu 54da gwamnatin ƙasar ta amince za ta biya.
A tataunawar da ƙungiyar ta yi da kwamitin ƙarin albashi da gwamnatin Najeriya ta kafa, kwamitin ya yi tayin biyan naira dubu 54 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan ƙasar.
Hakan, ƙari ne a kan naira 48,000 da kwamitin gwamnatin tarayyar ya yi tayin biya a zaman da ɓangarorin biyu suka yi cikin makon da ya gabata.
NLC ta ce ta yi watsi da tayin ne sakamakon halin matsin rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.
Ɓangarorin biyu za su sake zama a yau Laraba domin ci gaba da tattaunawar kan mafi ƙarancin albashi a ƙasar nan.
Tun da farko dai NLC ta ce tana so gwamnatin ƙasar ta biya naira 615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, la’akari da halin da ake ciki a ƙasar na ƙaruwar hauhawar farashi da karyewar darajar kudin ƙasar.

Leave a Reply