Ƙungiyar Masu Kiwon Kaji A Kano Ta Ƙara Farashin Ƙwai

Ƙungiyar masu kiwon kaji a jihar Kano ta sanar da ƙarin farashin kwai, sakamakon tashin gwauron zabin da abincin kaji yayi.

Ƙungiyar ta ce bayan nazari da ‘ya’yanta suka yi kan yadda suke tafiyar da sana’ar tasu, sun cimma matsayar sanar da sabon farashi, inda ta ƙara da cewa abincin kaji mai iganci a yanzu ya haura naira 11,000 a kan ko wanne buhu.

Shugaban ƙungiyar, dakta Usman ya ce idan ba su ƙara farashin ƙwan ba, zasu tashi babu riba.

Ya kuma jadadda cewa sabon farashin shawara ce da suka bai wa junansu, ba wai umarni ba.

Masu kiwon kajin sun ce babban abin da ake hada abincin kajin da shi, wato masara ta yi tsada, lamarin da ya sa wasu daga cikin su ke dakatar da aiki.

Leave a Reply