‘Ƙararraki sun yi wa kotun ƙolin Najeriya katutu’

Alƙalin alƙalan Najeriya, mai shari’a Olukayode Ariwoola ya ce shari’o’i sun yi wa kotun ƙolin ƙasar yawa, ciki kuwa har da waɗanda ba su taka kara sun karya ba.

Babban mai shari’ar ya bayyana haka ne a Abuja, lokacin wani taro na musamman na ƙaddamar da shekarar shari’a ta 2022 zuwa 2023, da kuma rantsar da manyan lauyoyi 63 na ƙasar.

A cewar alƙalin wasu daga cikin shari’o’in ba su cancanci a kai su kotun ta ƙoli ba.

Ya ce “akwai buƙatar a tunatar da ƴan Najeriya cewar ya kamata su daina yawan shigar da ƙararraki, a maimakon haka, su rinƙa bin wasu hanyoyin sulhuntawa domin rage wa kotuna nauyi.”

Ya ƙara da cewa “ƴan Najeriya, musamman ma ƴan siyasa ne waɗanda suka fi shigar da ƙara a faɗin duniya.”

A lokacin da yake bayani kan alƙaluma, mai shari’a Ariwoola ya ce akwai ƙararraki 6,884 da aka ɗaukaka zuwa kotun ƙoli waɗanda ba a yi aiki a kansu ba har yanzu.

Leave a Reply